in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Yandong: an kafa sabon tsarin raya yankin yammacin kasar Sin
2018-02-04 13:34:55 cri
Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong ta fada cewa, ya kamata a koyi tunanin Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, da tunanin taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, da aiwatar da manufofin raya fannin ba da ilmi, da horar da kwararru, da yin kirkire-kirkire, da kiwon lafiya, da inganta kimiyya da fasaha, da al'adu da sauransu don biyan bukatun jama'ar kasar. Ta bayyana hakan ne yayin da take yin bincike a birnin Chongqing dake yammacin kasar Sin a kwanakin baya cewa.

Haka zalika Liu Yandong, ta kai ziyara a jami'ar Chongqing da sauran kwalejoji, inda ta yi nuni da cewa, ya kamata a mai da sha'anin bada ilmi a matsayin aiki mai muhimmanci, da inganta jami'o'i da kwalejoji da kuma fannonin da aka koya a cikinsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China