in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta tsai da kudurin sake rage darajar kudin kasar
2018-02-05 10:41:24 cri
A ranar 4 ga wata, bankin tsakiya na kasar Sudan ya tsai da kudurin sake rage darajar kudin kasar, wato ya canja farashin musayar kudi tsakanin dallar Amurka da kudin kasar Sudan, inda a yanzu dallar Amurka 1 za ka kama kudin Sudan 30.

Kafin hakan kuma, gwamnatin kasar Sudan ta taba tsai da kudurin canja farashin musayar kudi tsakanin dallar Amurka da kudin Sudan daga dallar Amurka 1 zuwa kudin Sudan 6.7 zuwa dallar Amurka 1 kan kudin Sudan 18 tun daga watan Janairu na bana.

A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, za ta dauki matakai domin hana faduwar darajar kudin kasar, yayin da ta dauki matakai bisa dokokin kasar kan wadanda suke aikata laifin lalata yanayin kasuwar musayar kudade.

A watan Oktoba na shekarar 2017, kasar Amurka ta sauke takunkumin da ta kakaba wa kasar Sudan ta fuskar tattalin arziki, amma matakin bai ba da taimako ga kasar Sudan wajen hana raguwar tattalin arzikin kasar ba. A halin yanzu, ana iya samun kudin Sudan 41.7 kan dallar Amurka 1 a kasuwar bayan fage. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China