in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta takaita fitar da makamai zuwa Sudan ta Kudu
2018-02-03 14:06:57 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar jiya Jumma'a cewa, sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar Sudan ta Kudu, Amurkar za ta takaita fitar da makamai da sauran wasu kayayyaki zuwa ga gwamnatin kasar gami da kungiyoyin da ba sa ga maciji da gwamnatin.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert ya ce, Amurka ta nuna damuwa sosai game da rikice-rikice a Sudan ta Kudu, inda ya ce, ma'aikatarsa zata zartas da wasu gyare-gyare kan manufofin kasuwanci kan Sudan ta Kudu, da takaita fitar da makamai da sauran wasu kayayyaki zuwa ga bangarori daban-daban da suke rikici da juna. Heather Nauert ya kuma yi kira ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya azawa Sudan ta Kudu takunkumin hana jigilar makamai zuwa kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China