in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta damu game da kalubalen da ake fuskanta a Darfur
2018-02-01 09:31:04 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana damuwa game da kalubalen da yankin Darfur na Sudan yake fuskanta, duk da ingantuwar al'amuran tsaro da yanayin jin kai da aka samu a yankin.

A cikin wata sanarwar shugaba da Kairat Umarov, shugaban kwamitin sulhun majalisar na watan Janairu ya gabatar, mambobin kwamitin mai wakilai 15 sun ba da misali da kalubalen da ake fuskanta na magance yanayin da mutane miliyan 2.7 da suka rasa matsugunansu ke ciki a yankin na Darfur, inda suka yi kira ga gwamnatin Sudan da kasashen duniya da su hada kai wajen lalubo hanyoyin da za a magance halin da wadannan mutane ke ciki.

Haka kuma kwamitin sulhun ya damu matuka game da fadace-fadacen kabilanci dake faruwa a yankin, lamarin da kwamitin ya ce na iya zama wata kafa ta kara tayar da hankali a yankin.

Sai dai duk da ingantuwar yanayin tsaro da aka samu a yankin na Darfur, har yanzu ana ci gaba da keta hakin bil-Adama, ciki har da cin zarafi masu nasaba da jinsi.

Rahotanni na cewa, shekaru 6 tun bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar yankin Darfur a birnin Doha, har yanzu al'ummar Darfur din ba su gani a kasa ba. A don haka kwamitin sulhun MDDr ke nanata goyon bayansa ga wancan yarjejeniyar a matsayin hanya mafi dacewa ta cimma zaman lafiya a yankin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China