in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta janye jakadanta dake Amurka
2018-02-04 12:43:27 cri
Mai magana da yawun shugaban kasar Sudan ta kudu Ateny Wek Ateny, ya sanar da cewa, kasar ta janye jakadanta dake kasar Amurka, kwana guda bayan da gwamnatin Amurkar ta bada sanarwar kakabawa Sudan ta kudun takunkumin hana sayar mata da makamai.

Ateny ya ce, an baiwa jakadan kasar Garang Diing Akuong, umarnin ya gaggauta komawa kasarsa don ci gaba da tuntuba ba tare da yin wani karin haske ba. A watan Mayun shekarar 2015 ne Sudan ta kudun ta tura jakadanta zuwa Washington DC.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, Ateny ya ce, wannan wani tsari ne da kasar ke yi don tuntubar jakadanta. Amma ba shi da nasaba da batun takunkumin hana sayar da makaman da aka kakabawa kasar.

A ranar Juma'a ne gwamnatin Trump, ta sanar da kakabawa Sudan ta kudun takunkumin kin sayar mata da makamai, kuma ta bukaci kwamitin sulhun MDD da ya aiwatar da sanya takunkumin hana dukkan kasashen duniya sayarwa Sudan ta kudun makamai.

Amurkar ta kuma bukaci kungiyar tarayyar Afrika (AU), da kungiyar raya kasashen gabashin Afrika (IGAD), da su dauki mataki kan dukkan kasar dake neman wargaza shirin wanzar da zaman lafiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China