in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu dubu 800 ne ke zaune a kasar Sudan
2018-02-01 10:39:35 cri
MDD ta sanar da cewa adadin 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu dake zaune a kasar Sudan ya kai dubu 800

Noriko Yoshida, jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) a Sudan, ya sanar a lokacin wani taro game da batun 'yan gudun hijirar cewa, wasu majiyoyin sun ce yawan 'yan gudun hijirar ya zarta wannan adadi.

Ya ce wannan ya sa Sudan ta kasance kasa ta biyu mafi karbar bakuncin 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu a wannan shiyyar.

Mataimakin shugaban kasar Sudan Hassabo Mohamed Abdul-Rahman, ya bayyana a lokacin taron cewa, kasar Sudan ta jaddada matsayinta na karbar bakuncin 'yan gudun hijirar tare kuma da samar musu muhimman abubuwan bukatun rayuwa.

Kana ya sake yin kira ga MDD da sauran kasashen duniya masu bada agaji, da su sauya hanyoyin da suke bi wajen bayar da taimakon kudade don agazawa 'yan gudun hijirar wadanda kasar ke karbar bakuncinsu.

Kasar Sudan tana karbar bakuncin 'yan gudun hijira kimanin miliyan 2 daga kasashen Habasha, Eritrea, Chadi, Somalia, Jamhuriyar tsakiyar Afrika, Sudan ta kudu, Yemen da kuma Syria. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China