Shugaban 'yan tawayen bangaren arewaci Abdel Azizi al-Hilu wanda ya sanar da hakan a jiya Talata, ya ce wannan mataki wata dama ce ta kawo karshen rikicin Sudan cikin ruwan sanyi. A don haka ya umarci dukkan rundunonin soja dake karkashin kungiyar, da su martaba wannan kuduri.
Mahukuntan Sudan da kungiyar dai sun sha tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta daga lokaci zuwa lokaci a yankunan kudancin Kordofan da Bule Nile.
A ranar 3 ga watan Fabrairu mai kamawa ne ake saran za a koma teburin tattaunawar zaman lafiya tsakanin sassan biyu dangane da Kudancin Kordofan da Bule Nile a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Wata tawagar sasantawar kungiyar tarayyar Afirka(AU) karkashin jagoarcnin tsohon shugaban Afirka ta kudu Thabo Mbeki ne suke sa-ido a tattaunawa tsakanin sassan biyu. (Ibrahim)