Karkashin yarjejeniyar, gwamnatocin biyu sun cimma matsaya cewa bankin nan Exim na kasar Sin ne zai samar da rancen kudaden gudanar da aikin.
Ministan kudu da tsara tattalin arziki na kasar Sudan ta kudun Stephen Dhieu Dua, ya yabawa gwamnatin kasar Sin bisa irin taimakon da take cigaba da baiwa kasarsa na sake gina kasar wanda yaki ya daidaita.
Ya kara da cewa, suna kuma cigaba da tattaunawa da gwamnatin Sin, da kamfanonin kasar Sin da hukumomin kula da al'amurran kudi na kasar Sin don samar da kudaden gudanar da wasu ayyukan raya kasa a Sudan ta kudun.
Jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu He Xiangdong, ya bayyana cewa, da zarar aikin ya kammala, zai baiwa kasar Sudan ta kudu damar samun kudaden shiga a harkokin sufurin jiragen sama, kuma zai taimakawa kasar wajen kiyaye ikon sararin samaniyarta, da kiyaye 'yancin mallakar yankunan kasar.(Ahmad Fagam)