in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada tsohon kwamandan sojojin Zimbabwe mataimakin shugaban jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar
2017-12-24 12:48:58 cri

An nada Constantino Chiwenga, tsohon kwamandan askarawan kasar Zimbabwe mataimakin shugaban jami'yya kuma sakatare na biyu na jamiyyar Zanu-PF mai mulkin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar George Charamba shi ne ya tabbatar da nadin cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Asabar.

Charamba ya ce, Chiwenga, ya yi ritaya daga aiki a rundunar sojin kasar ne a makon jiya, bayan da ya jagoranci sojojin kasar wajen shiga tsakani wanda ya yi sanadiyyar yin murabus din tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a watan Nuwamba, kuma an nada shi a mukamin ne tare da ministan tsaron kasar kuma masanin dabarun yaki Kembo Mohadi.

Mohadi dai dan tsohuwar jamiyyar PF-Zapu ne, wanda marigayi tsohon mataimakin shugaban kasar Joshua Nkomo ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kan kasar tare da shugaba Mugabe na Zanu-PF a wancan lokaci, inda daga bisani aka kafa hadakar jami'yyar ta Zanu-PF.

Nadin mukaman biyu, zai sharewa jami'an biyu hanya na samun mukamin kujerar mataimakin shugaban kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China