Mnangagwa, ya bayyana tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe Robert Mugabe, a matsayin dan kishin Afrika na hakika, kana ya bukaci mambobin kasashen na AU da su kara karfafa dangantar zamantakewa da tattalin arziki a tsakaninsu.
Mnangagwa, yayi wannan tsakaci ne a lokacin da ya halarci taron sabon shirin raya cigaban Afrika (NEPAD), wanda aka gudanar a gefen taron kolin na AU karo na 30, wanda ke gudana a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.
Yace kasar Zimbabwe tana matukar alfahari da kasancewarta daya daga cikin wannan babbar kungiya wanda ta kasance tamkar iyali ne guda, ya kara da cewa, kasarsa a shirye take ta marawa dukkan ayyukan kungiyar ta AU baya don cigaban nahiyar Afrika.
Mnangagwa ya bayyana aniyar gwamnatinsa na yin aiki tare da dukkannin kasashen Afrika, a bisa tsarin daidaiku da kuma tsarin gamayyar kasashen.