Mnangagwa, wanda a halin yanzu yake ziyarar aikinsa ta farko a kasar Afrika ta kudu, kuma ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasashen ketare tun bayan da ya dare kujerar shugabancin kasar ta Zimbabwe a ranar 24 ga watan Nuwambar 2017
Da yake jawabi a gaban dandazon 'yan kasar Zimbabwean a Pretoria na kasar Afrika ta kudu, Mnangagwa ya ce, lokaci ya yi ga 'yan kasar dake zaune a kasashen waje za su koma gida.
Miliyoyin 'yan kasar Zimbabwe ne suka tsere zuwa kasashen waje, mafi yawansu sun kaura ne zuwa kasar Afrika ta kudu a tsawon lokacin mulki mista Mugabe na shekaru 37.
Mnangagwa ya ce 'yan kasar Zimbabwean dake zaune a Afrika ta kudu ya kamata su koma gida, kana su yi amfani da irin kwarewar da suka samu a makwabciyar kasar don sake gina tattalin arzikin kasar ta Zimbabwean da kuma gina cigaban kasarsu ta asali.
Tun a ranar Alhamis ne, Mnangagwa ya gana da shugaba Zuma, kuma dukkannin shugabannin biyu sun sha alwashin yin hadin gwiwa don gina tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)