in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta nuna damuwa game da kalaman shugaba Trump
2018-01-17 20:24:22 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Zimbabwe ta fidda wata sanarwa dake tir da kalaman da aka rawaito shugaban Amurka Donald Trump na yi, na cin mutuncin kasashen Afirka.

Sanarwar da aka wallafa a jaridar "The Herald" ta yau Laraba, ta ce kalaman na shugaba Trump na da ciwo, kuma nuna wariya ne ga kasashen Afirka, kana sam ba su dace da yanayin ci gaban duniya na yanzu ba.

Sanarwar ta kara da cewa, kalaman shugaban na Amurka sun girgiza kasar Zimbabwe, tare da fusata al'ummar ta.

Gwamantin Zimbabwe ta ce za ta bi sahun takwarorin ta na nahiyar Afirka da sauran wadancan kalamai suka shafa, wajen yin tofi Allah tsine ga kalaman kaskantarwa da shugaba Trump ya furta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China