in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a kafa gwamnatin hadaka da jam'iyyar adawa a Zimbabwe ba, in ji shugaban kasar
2018-01-06 13:10:19 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar ba zata kafa gwamnatin hadaka tare da jam'iyyar adawa ta MDC ba.

Da safiyar wannan rana, shugaba Mnangagwa ya kai ziyara a gidan shugaban jam'iyyar MDC, kana tsohon firaministan kasar Morgan Tsyangirai, inda suka yi shawarwari a sirri.

Kuma, bayan shawarwarin da suka yi, Mr. Mnangagwa ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, a halin yanzu, babu bukatar a kafa gwamnatin hadaka tsakanin jam'iyyar mai mulkin kasar da jam'iyyar adawa, kasancewa nan da 'yan watanni masu zuwa ne, za a fara babban zaben shugaban kasa a Zimbabwe.

A tsakanin shekarar 2009 da shekarar 2013, jam'iyyar ZANU-PF da jam'iyyar MDC sun taba kafa gwamnatin hadin gwiwa, kuma an mai da dan takarar jam'iyyar ZANU-PF Robert Mugabe a matsayin shugaban gwamnatin, yayin da dan takarar jam'iyyar MDC Morgan Tsyangirai ya kasance a matsayin firaministan kasar.

Haka kuma, a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, an zabi Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe, bayan tsohon shugaba Robert Mugabe ya yi murabus. Mr. Mnangagwa zai kuma ci gaba da gudanar da ayyukan shugaban kasa har zuwa babban zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar bana, amma, a halin yanzu, ba a fidda daidai lokacin yin babban zaben shugaban kasar ta Zimbabwe ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China