Jakadan kasar Sin dake Zimbabwe Huang Ping, ya taya mahalarta bakin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin, da yi musu bayani kan al'adun gargajiya da suka jibinci wannan gagarumin biki wato bikin bazara. Huang ya ce, shekarar da ta shude, shekara ce dake da matukar muhimmanci ga Sin da Zimbabwe. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi nasarar kira babban taron wakilanta karo na 19 a Beijing, kuma tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin ya shiga sabon yanayi. Ita ma Zimbabwe ta zabi sabon shugabanta. Jakadan Huang ya ce, bayan da Mnangagwa ya hau karagar mulkin kasar, gwamnatin kasar Sin ta tura wakilinta na musamman zuwa kasar ba tare da wani jinkiri ba, lamarin da ya shaida irin kudirin gwamnatin kasar Sin na karfafa hadin-gwiwa da raya dangantaka tare da Zimbabwe.
Mista Huang ya kara da cewa, a shekara ta 2018, za'a iya samun kyakkyawar makoma wajen raya huldodin Sin da Zimbabwe. Shugaban Zimbabwe Mnangagwa zai ziyarci kasar Sin a watan Afrilu, kana kuma za'a kira babban taron dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato taron FOCAC a watan Satumba a Beijing. Babu tantama hadin-gwiwar Sin da Zimbabwe zata kara samar da alfanu ga al'ummar kasashen biyu.(Murtala Zhang)