in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu
2017-11-12 13:30:55 cri
Kungiyar sa kaimi ga yin ciniki a tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin da bankin kasar Sin da majalisar masana'antu da cinikayya ta kasar Afirka ta Kudu, sun gudanar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu a ranar 10 ga wata, inda mahalartar taron suka tattauna kan hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin hadin gwiwarsu ta tattalin arziki da cinikayya.

A gun taron, karamin jakadan Sin dake birnin Johannesburg Ruan Ping ya bayyana cewa, ana raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a shekarun baya baya nan, kasar Afirka ta Kudu ta riga ta zama kasa mafi girma ta abokiyar ciniki ta kasar Sin, kana ta zama muhimmin wurin zuba jari da yawon shakatawa na kasar Sin.

Shugaban reshen Johannesburg na bankin kasar Sin Cheng Jun, ya bayyana cewa, tare da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da hadin gwiwar Sin da Afirka ta Kudu, babu shakka za a shiga sabon matsayi na hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya a nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China