in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya jaddada kudurinsa na sake fasalin tsarin tattalin arziki tun daga tushe
2017-11-10 12:46:17 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya bukaci al'ummar kasar su fuskanci gaskiyar cewa, sake fasalin tsarin tattalin arziki na da muhimmanci ga samun ci gaba na bai daya.

Jacob Zuma, ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa, a ko wace kasa, dole ne galibin al'umma su taka rawa a harkokin tattalin arziki, sai dai ba haka abun yake a kasar ba, saboda wariyar launin fata da har yanzu wasu suka zabi su musanta.

Ya jaddada cewa, sake fasalin tattalin arziki tun daga tushe, manufa ce ta gwamnati da ta samo asali daga Jam'iyyar ANC mai mulki, amma ba daga wajen kasar ba kamar yadda ake yada jita-jita

A shekarar 2012 ne jam'iyyar ANC ta yanke shawarar ba batun sauya fasalin tattalin arziki muhimmanci a matsayin wani mataki na tabbatar da daidaito, wanda ya kunshi muhimman matakai da dabaru da za su shafi zamantakewa da tattalin arziki da kuma demokuradiyya.

Shugaba Zuma ya ce, daga nan ne kuma aka ayyana sauya fasalin zamantakewa da tattalin arziki tun daga tushe a matsayin abu mafi muhimmanci a shekarar 2017 da ta 2018. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China