A wannan rana, mahalarta taron suka zabi sabbin shugabannin jam'iyyar, baya ga Cyril Ramaphosa da aka zaba a matsayin shugaban jam'iyyar, an kuma zabi David Mabuza a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar, Gwede Mantashe a matsayin jagoran kasa, yayin da aka zabi Ace Magashule a matsayin babban sakatare.
Mr. Ramaphosa dai shi ne zai maye gurbin shugaban jam'iyyar ANC na yanzu Jacob Zuma, a sa'i daya kuma, Jacob Zuma zai ci gaba da kasancewa shugaban kasar har zuwa shekarar 2019, wato lokacin da za a gudanar da babban zaben shugaban kasar Afirka ta Kudu.
Cyril Ramaphosa mai shekaru 65 ya lashe zaben mataimakin shugaban jam'iyyar ANC a watan Disamba na shekarar 2012. A watan Mayu na shekarar 2014 kuma, aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu. (Maryam)