in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin harkokin sadarwa a Afirka ta Kudu
2017-11-08 13:52:38 cri
Jiya Talata ne aka bude bikin baje kolin harkokin sadarwa mafi girma a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu. A yayin bikin na kwanaki 3, kamfanonin kimiyya da fasaha da na harkokin sadarwa kimanin 400 za su nuna sabbin fasahohinsu da kuma na'urori, ciki har da wasu kamfanonin kasar Sin.

Ko da a cikin shekarun baya bayan nan, kasashen Afirka sun dukufa wajen raya harkokin intanet, amma ana fuskantar wasu matsaloli wajen aiwatar da ayyukan da abin ya shafa, kamar yawan jahilai a kasashen Afirka, da karancin gina ababen more rayuwa da kuma tsadar kudin yin amfani da intanet da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China