in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe daban daban sun taya Sinawa murnar bikin bazara
2017-01-29 13:02:05 cri
A yayin bikin bazara wato sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shugabanni da kusoshin wasu kasashe da dama daya bayan daya sun taya al'ummar Sinawa murnar shiga sabuwar shekarar zakara.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya aika da sakon fatan alheri ta ofishinsa, inda ya bayyana fatansa na ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A wasikar fatan alheri da firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacke ya aika, ya ce, gwamnatin kasarsa ta nuna yabo sosai kan kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren, shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya yi godiya da goyon baya da taimakon da kasar Sin ta samar wa kasarsa, ya ce, kasar Tanzania za ta goyi bayan Sin a batun tekun kudancin Sin.

Baya ga haka, shugabannin kasashen Brazil, Australia, Malta, Myanmar, Fiji da sauransu su ma sun aika da sako ko wasika don nuna fatan alheri ga daukacin al'ummar Sinawa game da murnar bikin bazarar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China