in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shagulgulan bikin Bazara a Najeriya
2017-01-29 12:23:58 cri

A jiya ne Sinawa da ke zaune a Najeriya suka shirya shagulgulan murnar bikin bazara na bana wato shekarar Zakara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.

A Abuja, bikin wanda ofishin jakadancin kasar Sin da ke Najeriya ya shirya, ya samu halartar Sinawa da jami'an Najeriya da kuma dalibai da dama. Wannan biki yana daya daga cikin bukukuwan da al'ummar Sinawa mazauna Najeriya suka shirya don murnar bikin Bazara na bana.

Mahalarta bikin sun kashe kwarkwatan ido a cibiyar al'adun gargajiyar kasar Sin da ke Abuja, fadar mulkin Najeriya inda suka kalli raye-rayen al'adun gargajiyar kasashen Sin da Najeriya daban-daban wanda daliban sakandaren 'yan mata ta gwamnati dake garin Dutse a jihar Jigawa suka shirya.

A jawabinsa jakadan kasar Sin da ke Najeriya Zhou Pingjian ya shaidawa manema labarai cewa, shagulgulan wata alama ce ta fatan alheri a sabuwar shekarar.

Tun da farko a sakonsa na fatan alheri da ya aikawa daukacin Sinawa da ke Najeriya da sauran sassan duniya game da bikin na Bazara, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bikin a matsayin bikin gargajiya mafi muhimmanci ga al'ummar Sinawa,wanda ke jaddada fa'idar haduwar iyali,akidar da kasashen biyu suke alfahari da ita.

Bikin Bazarar dai ya samu karbuwa sosai a manyan biranen Najeriya sakamakon yadda Sinawa da ke Najeriya ke shirya kasaitaccen biki a kowace shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China