
Jiya Talata ne Raila Amolo Odinga, tsohon firaministan kasar Kenya kuma shugaban jam'iyyar 'yan hamayya ta NASA ya rantsar da kansa a matsayin "shugaban jama'a" a gaban dubban masu goyon bayansa a birnin Nairobi, hedkwatar kasar.
A watan Agustan bara ne, aka gudanar da zaben shugabancin kasar Kenya, inda Uhuru Kenyatta ya sake lashen zaben. Sai dai jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya ki amincewa da sakamakon zaben, ya kuma kai kara a babbar kotun kasar, inda ya bukaci a sake gudanar da zaben. Daga baya, babbar kotun ta yanke hukuncin soken sakamakon zaben.
A ranar 26 ga watan Oktoban bara ne aka sake gudanar da zaben shugabancin kasar ta Kenya, inda Uhuru Kenyatta ya sake lashen zaben. Ko da yake Odinga ya sake kin amincewa da sakamakon zaben, amma babbar kotun kasar ta amince da sakamakon zaben. Daga baya Odinga ya sha yin shelar cewa, zai rantsar da kansa a matsayin "shugaban jama'a". (Tasallah Yuan)




