in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kafa cibiyar samar da kayakin kumfyuta a Kenya
2018-01-04 10:53:39 cri
Kamfanin kasar Sin mai samar da kayakin kumfyuta wato Anycolor Computer Co.LTD, na shirin kafa wata masana'antar sarrafa kayayyaki da kuma wata cibiyar kasuwanci ta gabashin Afrika a kasar Kenya a bana.

Anycolor babban kamfani ne dake aikin bincike da samarwa tare da sarrafa kayakin kumfyuta.

Xu Huanwen, Babban Manajan Arecolor wanda reshe ne na kayakin da Anycolor ke samarwa a Kenya, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, suna son kafa masana'antar da darajarta ta kai dala miliyan 10 domin samar da kayayyakin na'urar buga takardu da suka hada da kurtun tawada da tawada da madaukan kurutu da kuma batirin tafi da gidanka.

Xu Huanwen ya ce suna duba wurin da yafi dacewa da kafa masana'antar a yankunan harkokin tattalin arziki na musammam, wanda ke da dukkan kayakin more rayuwa da ake bukata.

A yanzu, Arecolor na da masana'antu biyu a kasar Sin, inda na kasar Kenya zai zama na farko a ketare.

Ana sa ran cibiyar za ta samar da aikin yi ga 'yan asalin yankin 300 tare da samar da madaukan kurtun tawada miliyan 3.6 da madaukan tawada miliyan 6 da kuma batirin tafi da gidanka miliyan 2 a duk shekara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China