in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren adawa na kasar Kenya ya dage ranar rantsar da shugabanninsa
2017-12-11 10:56:53 cri
Hadakar jam'iyyun adawa ta kasar Kenya wato NASA, ta dage ranar da ta shirya rantsar da shugabanninta, sai dai ta lashi takobin kara daura damarar ganin ba ta russunawa Gwamnatin Shugaban kasar Uhuru Kenyatta ba.

A baya, NASA ta shirya gudanar da bikin rantsuwar ne a ranar da kasar ke bikin samun 'yancin kai, inda za ta rantsar da Raila Odinga a matsayin shugaban kasa da Kalonzo Musyoka a matsayin mataimaki.

Shugabancin Jam'iyyar ya tabbatarwa magoya bayansa cewa, jam'iyyar za ta ci gaba da fafutukar tabbatar da adalcin zabe ta hanyar ganin bata russunawa Gwamnatin kasar ba.

Ana ta samunn matsin lamba daga abokan huldar Kenya na kasashen yammaci, domin NASA ta dakatar da rantsuwar ta kuma mai da hankali ga hawa teburin sulhu da shugaba Kenyatta.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata, sai da shugabannin addini da na kasuwanci da jakadun kasashen waje karkashin jagorancin jakadun Amurka da Birtaniya suka gana da shugabannin NASA a birninn Nairobi, suna masu bukatar NASA ta sake nazarin matsayarta, kana ta yi yukurin sulhuntawa da shugaba Kenyatta.

Sai dai Raila Odinga ya dage kai da fata cewa bikin zai gudana, inda a ranar Asabar, shugaban kasar ya ce ba zai hau teburin sulhu ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China