Bisa gayyatar da jam'iyyar Jubilee ta kasar Kenya ta yi mata, tawagar wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta ziyarci Kenya daga ranar 24 zuwa yau Jumma'a 26 ga wata, inda ta yi wa jam'iyyar Jubilee da sassa daban daban na Kenya cikakken bayani kan ruhun taron JKS karo na 19 da muhimman sakamakon da aka samu a yayin taron, kana ta yi bayani kan tunanin Xi Jinping na gurguzu mai halin musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, tare da gabatar da kyawawan dabarun JKS game da kara karfin ci gaban jam'iyyar. (Tasallah Yuan)