in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta hana manyan motocin fasinja masu yin doguwar tafiya yin tafiye tafiye cikin dare
2018-01-01 12:23:59 cri

Ranar 31 ga watan Disamban bara, hukumar kare hadurra ta kasar Kenya ta sanar da cewa, tun daga wannan rana, an hana manyan motocin fasinja masu yin doguwar tafiya yin tafiye tafiye da dare a duk fadin kasar, a wani mataki na rage abkuwar hadurran mota da dare.

Bisa wannan umurni, manyan motocin fasinja masu yin doguwar tafiya suna iya tafiye tafiye daga karfe 6 na safe zuwa 7 na dare a kowace rana. Da misalin karfe 3 saura minti 10 na safiyar ranar 31 ga watan Disamban bara ne aka sanar da wannan umurni, a kuma wannan lokaci ne wata motar fasinja ta yi karo da wata motar dakon kaya yayin da take kokarin wuce wata motar ta daban, a kan hanyar da ke tsakanin garin Nakuru da garin Eldoret a yammacin kasar, inda mutane a kalla 36 suka rasa rayukansu.

Ana dai samun hadurran mota da yawa a kasar Kenya, saboda hanyoyi marasa fadi dake da yawa a sassa daban daban, wadanda kuma ba a kula da su yadda ya kamata. Kana kuma, su kansu manyan motocin fasinja da ake amfani da su ba su da inganci sosai. Baya ga daukar fasinjoji fiye da yadda aka kayyade, sa'an nan sau da yawa su kan yi gudun wuce sa'a.

Bisa kididdigar da hukumar kare hadurra ta kasar ta fitar, kimanin mutane dubu 3 ne suke rasa rayukansu, sakamakon hadarin mota a kowace shekara a kasar ta Kenya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China