Jami'in ya bayyana wa 'yan jarida cewa, motar dake dauke da sojojin ta taka nakiyar da aka binne a gefen titi ne. Rundunar 'yan sandan yankin tana zaton dakarun kungiyar Al-Shabaab ne suka binne nakiyar. An dai riga an tura wani rukunin sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru don ganin an kama maharan
Salah ya kara da cewa, an kai gawawwakin sojojin da suka mutu a sakamakon harin da ma sojoji da suka ji rauni zuwa asibitin dake birnin Nairobi domin yi musu magani. (Zainab)