in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana taimakawa Kenya wajen horas da ma'aikatan kasar
2017-12-22 13:45:57 cri
Jiya Alhamis, an kira taron mu'amala a tsakanin ma'aikatan da suka samun horaswa a kasar Sin, a ofishin mashawarcin jakada mai kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya. Kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, ya zuwa watan Nuwanba bana, gaba daya 'yan kasar Kenya 563 sun taba halartar shirin ba da horaswa na kasar Sin bisa fannonin ayyukan gona, da kiwon dabbobi, da sha'anin kudi, da harkokin masana'antu da kuma kiwon lafiya da dai sauransu.

A yayin taron, mashawarcin jakada Guo Ce ya ba da jawabi cewa, shirin ba da horaswa ga 'yan kasashen ketare na kasar Sin, ya zama muhimmiyar hanya ta kasar wajen karfafa mu'amala tsakanin al'ummomin kasar Sin da kasashen ketare. Kuma, ana da imanin cewa, tabbas masu samun horon za su kara ilimi game da harkokin siyasa, tattalin arziki da kuma al'adu na kasar Sin.

A halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya tana bunkasa cikin yanayi mai kyau, a nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taikamawa kasar Kenya, wajen raya sassan sarrafa albarkatun kwadago, in ji jami'in.

Shugaban cibiyar sarrafa albarkatun kwadago ta ma'aikatar harkokin ba da hidima ga al'umma, matasa da jinsi ta kasar Kenya Dennis Mutahi, ya nuna yabo matuka kan sakamakon da aka samu bisa horaswar da 'yan kasar suka samu, ya kuma nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin, domin kyawawan damammakin da ta samar wa al'ummomin kasar Kenya.

Haka zalika, ya ce, ya kamata a aiwatar da sakamakon da aka samu a kasar Kenya yadda ya kamata, domin biyan bukatun al'ummomin kasar, wajen kara saninsu da kuma kyautata kwarewarsu wajen gudanar da ayyuka daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China