in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Afirka sun musanta rahotan dake cewa Sin tana sa ido kan AU
2018-01-30 11:13:49 cri

Jiya Litinin ne, aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU karo na 30 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, a yayin taron, wasu jami'an kasashen Afirka sun musanta rahoton da wata kafar yada labarai ta kasar Faransa take yayatawa wai, kasar Sin tana sa ido kan kungiyar AU.

A jiya ne, firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya bayyana a hedkwatar kungiyar AU cewa, kasar Sin ba ta sa ido kan kungiyar AU, kuma rahoton ba na gaskiya ba, a halin yanzu, kasar Sin da kungiyar AU suna da dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

Shi ma shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi bayan kammala taron kolin kungiyar cewa, bai ga wata alamar sa ido kan ginin kungiyar AU ba, kuma dangantakar dake tsakanin kungiyar AU da kasar Sin tana bunkasa cikin yanayi mai kyau.

A nasa bangare, shugaban tawagar wakilan kasar Sin dake kungiyar AU Kuang Weilin ya jaddada cewa, taimakon da kasar Sin ta baiwa kungiyar AU na gina babban ginin kungiyar, wani babban goyon baya ne da kasar Sin ta nuna wa kungiyar, kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen raya hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar AU yadda ya kamata. Kuma wannan rahoto ba zai gurgunta alakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU ba, domin hadin gwiwar bangarorin biyu ta dace da yanayin da duniya ke ciki, kuma za a ci gaba da karfafa huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, har ma da kungiyar AU. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China