in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashe tashen hankula da sauyin yanayi sune manyan kalubalolin dake haifar da yunwa da talauci a Afrika, inji MDD
2018-01-28 13:39:27 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana matsalolin yawaitar tashin hankali da sauyin yanayi a matsayin manyan dalilan dake haifar da karuwar yunwa da talauci a kasashen Afrika.

Guterres, wanda ya gabatar da jawabi a wani taro game da yadda za'a kawo karshen yunwa a Afrika wanda ya gudanar a ranar Asabar a yayin taron koli na kungiyar tarayyar Afrika karo na 30 a kasar Habasha, ya bayyana cewa, Afrika na sahun gaba a shiyyoyin duniya da suka fi fama da matsalar yunwa, ya jaddada bukatar daukar matakan kawo karshen tashe tashen hankula da magance matsalar sauyin yanayi domin samun nasarar kawo karshen matsalar yunwa a nahiyar.

Guterres, ya lura cewa matsalar yunwa tafi kamari ne a kasashen da rikici ya daidaita, inda matsalar ta ninka har sau biyu, yace matsalar sauyin yanayi kamar gurbacewar muhalli, da faduwar farashin kayan amfanin gona da dabbobi, da matsalar yake yake duka nada nasaba da matsalolin dake addabar nahiyar.

A cewar babban jami'in MDDr, mafi yawan mutanen dake fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki suna kasashen Afrika ne wadanda yaki ya daidaita su.

Don hakan ya bukaci gwamnatocin kasashen Afrika dasu tsaya tsayin daka, kana kungiyar AU da MDD su kara azama wajen aikin wanzar da zaman lafiya da kare hakkin dan adam domin samun nasarar kawar da talauci da yunwa a Afrika.

A cewar mista Guterres, tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin bil adama a Afrika zasu samar da wani kyakkyawn yanayi na yiwuwar samun dauwwamamman cigaba, kuma zasu zama wani jigo na yaki da matsalar yunwa.

Alpha Conde, shugaban kasar Guinea, kuma shugaban taron kolin AU na wannan karo, ya nanata cewa matsalar yunwa da talauci tana matukar shafar al'ummar Afrika, kuma har ma tana iya shafar ingancin rayuwarsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China