in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su amince da yarjejeniyar kare hakkin tsofaffi
2018-01-29 20:43:44 cri
Masu rajin kare hakkokin tsofaffi sun yi kira ga shugabannin nahiyar Afirka, da su gaggauta sanya hannu tare da amincewa da kudurin da ya tanaji kare hakkokin tsofaffin dake rayuwa a nahiyar.

Masu wannan bukata dai sun gudanar da tattaki zuwa harabar taron kolin shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU dake gudana a birnin Addis Ababa a Litinin din nan, inda suka gabatar da bukatar matsin lamba game da gaggauta aiwatar da wannan kuduri.

Cikin wata sanarwa da suka gabatar, masu rajin kare bukatun tsofaffin sun ce kudurin da aka gabatar yayin taron kungiyar na shekarar 2016, ya tanaji hanyoyin kare daraja da kimar tsofaffin nahiyar Afirka. To sai dai a cewar daraktan yankin Afirka na kungiyar "HelpAge International" Prafulla Mishra, ya zuwa yanzu kasashe 4 kacal ne suka sanya hannu kan wannan kuduri, kana ba wata kasa da ta tabbatar da shi a hukunce.

Mr. Mishra ya ce hakan wani koma baya ne ga tsoffin dake rayuwa a Afirka, ya kuma saba wa burin da ake da shi na kare martabar tsaffin, ganin yadda suke fama da wariya, da watsi da al'amuran su, tare da muzguna musu, a wasu lokutan ma hadda cin zarafin su ta fuskar zamantakewa a tsarin al'adu da siyasa.

A watan Janairun shekarar 2016 ne taron AU ya amince da kudurin kare darajar tsofaffi, wanda ya tanaji karfafa tsare tsare ko manufofi na shari'a, wadanda za su kara kyautata rayuwar tsofaffin dake raye a nahiyar Afirka baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China