A yayin taron, mambobin kungiyar AU sun tattauna game da matsalar cin hanci da rashawa, inda suka tsara wasu matakan warware wannan matsala. Haka kuma kasashen kungiyar sun sanar da kafa kasuwar sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen Afirka a hukunce, da jaddada muhimmancin hadin gwiwar mambobin kungiyar wajen yaki da ta'addanci.
A jawabinsa yayin rufe taron, sabon shugaban kungiyar, kana shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana cewa, an tsai da wasu muhimman kudurori a yayin taron kolin kungiyar AU na wannan karo, wadanda za su taimaka ga bunkasuwar kasashen Afirka a nan gaba. Haka kuma, ya ce, ya kamata kasashen Afirka su hada kai don karfafa dunkulewar kasashen Afirka waje guda.
A nasa jawabin, shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki ya bayyana cewa, yaki da cin hanci da karbar rashawa shi ne babban nauyin dake wuyan kasashen Afirka, lamarin da ke damun al'ummomin kasashen kwarai da gaske. (Maryam)