Babban taken taro na wannan karo shi ne, "Cimma nasarar yaki da cin hanci da rashawa, hanya mafi dacewa ta farfadowa da kasashen Afirka". A kwanaki biyu na taron, shugabanni mambobin kungiyar za su tattauna batutuwan yiwa kungiyar gyaran fuska,da batun dunkulewar kasashen Afirka da kuma yaki da cin hanci da karbar rashawa da dai sauransu.
A jawabinsa yayin bikin bude taron, shugaban hukumar zartarwar kungiyar AU Moussa Faki ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta yiwa kungiyar AU kwaskwarima, domin kara karfin kungiyar na inganta dunkulewar kasashen nahiyar, hanya mafi dacewa don neman bunkasuwar kasashen Afirka baki daya.
Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, an sami babban ci gaba a matakin farko na shawarwarin kafa yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afirka, kuma ana sa ran zartas da yarjejeniyar yankin ciniki cikin 'yanci a taron kolin kungiyar AU na wannan karo. A sa'i daya kuma, a yayin taron ne, ake fatan bude kasuwar sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen Afirka. Haka kuma ya ce, ya kamata mambobin kungiyar su mai da hankali kan batun yaki da cin hanci da karbar rashawa, domin hana fitar da kudaden da aka sata ba bisa doka ba daga nahiyar Afirka zuwa ketare. (Maryam)