Mr. Gheit ya kara da cewa, kungiyar LAS tana mai da hankali sosai kan dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kungiyar AU, kuma a nan gaba, za ta dukufa wajen karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, kasashen Larabawa da kasashen Afirka suna fuskantar matsalolin tashe-tashen hankula, a don haka ya kamata su dukufa tare da yin hadin gwiwa domin warware wadannan matsalolin yadda ya kamata.
Ya kuma jaddada cewa, kungiyar LAS da kungiyar AU za su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu, sa kuma hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci. (Maryam)