in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin kasa da kasa na hanyar siliki na shekarar 2017 a kasar Sin
2017-06-04 13:30:43 cri
Jiya ranar Asabar a birnin Xi'an na kasar Sin, aka bude bikin baje kolin kasa da kasa na hanyar siliki na shekarar 2017, da dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa na zirin tattalin arzikin hanyar siliki, wanda ya samu halartar mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, a yayin jawabin da ya yi, ya jaddada cewa, shawarar 'Ziri daya hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wani babban aiki ne na kafa makomar bai daya ta dan Adam, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasashen dake kan hanyar siliki, don amfani da damar tabbatar da ra'ayin bai daya da aka cimma da nasarorin da aka samu a wajen dandalin tattaunawar koli na hadin kan kasa da kasa, da nufin daga matsayin hadin kan tattalin arziki da cinikayya da zuba jari zuwa wani sabon mataki, ta yadda za a kara samar da gajiya ga jama'ar kasashen dake kan hanyar silikin

Baya ga haka, Wang ya nuna cewa bikin baje kolin, ba kawai ya kasance wani dandalin dake inganta yin cudanya da samun cigaba tare a tsakanin yankunan dake gabashi da tsakiya da yammacin kasar Sin ba ne, har ma zai karfafa hadin kai a tsakanin Sin da kasashen dake kan hanyar tattalin arziki ta siliki a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Yana fatan bangarori daban daban zasu yi amfani da wannan tsari don yin cudanya da cimma ra'ayin bai daya, da gudanar da hadin kai, don kara samun moriya tare.

Kana Wang ya jaddada cewa, kasarsa na fatan kara bude kasuwa da juna tare da kasashen dake kan hanyar siliki, da zurfafa hadin kai a tsakanin hukumomin kwastan da binciken ingancin kaya, da mai da hankali kan wasu muhimman birane da ayyukasu, da kuma karfafa zuba jari da hadin kai a fannin samar da kaya da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China