in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta kaddamar da shirye shirye 3 da za su taimaka wajen dunkulewar nahiyar Afirka
2018-01-26 09:29:40 cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya ce kungiyar za ta kaddamar da wasu shirye shirye guda uku wadanda za su taimakawa manufar dunkulewar nahiyar waje guda.

Moussa Faki Mahamat wanda ya bayyana hakan yayin kwarya kwaryar taron kwamitin zartaswar kungiyar karo na 32 da ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya ce shirye shiryen sun hada da na samar da yankin ciniki maras shinge na nahiyar ko CFTA a takaice, da shirin baiwa al'ummar nahiyar zarafin sufuri tsakanin sassan nahiyar ba tare da wani kaidi ba, sai kuma aiwatar da yarjejeniyar Yamoussoukro wadda ta shafi samar da kasuwar bai daya da 'yantar da kasuwannin sufurin jiragen saman nahiyar.

Hukumar dake lura da tattalin arziki ta kungiyar ko UNECA a takaice, ta yi hasashen cewa, tsarin CFTA zai iya bunkasa hada hadar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar Afirka da kusan kaso 53.2 bisa dari ta hanyar kau da kudaden harajin shigar da kayayyaki, za kuma a iya samun ninkin hakan idan aka kau da karin shingaye na sauran sassan da ba su jibanci biyan haraji ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China