in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Tattalin arzikin Afrika zai bunkasa a 2018
2018-01-26 09:56:15 cri
Wata jami'ar MDD ta bayyana cewa, ana sa ran tattalin arzikin Afrika zai karu da kashi 3.5 bisa 100 a wannan shekarar ta 2018, sama da kashi 3.2 bisa 100 da aka samu a shekarar 2017.

Da take jawabi a taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, karo na 30 dake gudana a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Vera Songwe, sakatare janar ta hukumar tattalin arziki ta MDD game da kasashen Afrika (UNECA), ta bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin na Afrika ya ta'allaka ne da yawan bukatar da ake da shi na kayayyaki daga waje da kuma kwarya-kwaryar karuwar farashin kayayyakin da za'a samu.

Haka zalika, karuwar tattalin arzikin zai samu ne sakamakon cigaban da za'a samu a cikin gida wanda ya hada da maido da ayyukan hako mai a kasashen Afrika masu yawa da kuma tagomashin da za'a samu a fannin arzikin man a shekarun 2018 da 2019 a manyan kasashen nahiyar masu arziki da suka hada da Masar, Najeriya da Afrika ta kudu.

Sai dai kuma, ta ce karuwar tattalin arzikin ba zai wadaci nahiyar ba wanda adadin al'ummarta za su karu zuwa sama da mutane biliyan guda, kashi 70 bisa 100 na yawan jama'ar matasa ne.

Ta ce, ko da yake, matsayin talauci na raguwa, amma har yanzu alkaluman sun kai kashi 40 bisa 100 a nahiyar. Don haka, akwai bukatar rubanya kokari wajen fito da tsare tsare, da ingantaccen tsarin gudanar da tattalin arziki da bunkasa cigaban nahiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China