Muchanga Albert ya yi kiran ne yayin wani taron zantawa da manema labarai, a gefen taron shugabannin kungiyar karo na 30 da yanzu haka ke gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Ya ce nahiyar na bukatar dokoki da tsare tsare, wadanda za su share fagen cin gajiya daga fannin hakar ma'adanai yadda ya kamata.
Kungiyar AU ta sha bayyana nahiyar Afirka a matsayin wadda ke sahun gaba wajen fidda ma'adanai da tarin albarkarun kasa, amma kuma har yanzu tana fuskantar karancin tsarin binciken yanayin karkashin kasa, wanda hakan ke tauye gajiyar da nahiyar ke iya samu daga albarkatun na ta.(Saminu Alhassan)