in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya bukaci gamayyar kasa da kasa su hana yaduwar kiyayya a kasashen duniya
2018-01-27 13:26:25 cri
Jiya Jumma'a, babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya gabatar da jawabi gabanin zuwan ranar tunawa da mummunan kisan gilla mafi muni a duniya, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su yi hadin gwiwa wajen hana yaduwar kiyayya a kasashen duniya.

Ranar 27 ga watan Janairu na kowace shekara, rana ce da aka ware a matsayin ranar tunawa da kisan gilla mafi muni ta duniya.

Babban magatakardan MDDr ya ce, a wannan rana, MDD ta nuna juyayi ga Yahudawa kimanin miliyan 6 wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kisan kiyashi mafi muni a tarihi, da ma sauran mutanen kasa da kasa wadanda suka rasu a wancan lokaci mai cike da tashe-tashen hankula.

Ya kara da cewa, duk da kawo karshen yakin duniya na biyu da aka yi, amma har yanzu, ana ci gaba da fuskantar matsalar nuna kiyayya kan addinin Yahudawa, da ma sauran matsalolin da abin ya shafa.

Shi ya sa, Mr. Guterres ya jaddada cewa, dukkan mutanen kasa da kasa suna da nauyin hana tashin rikice-rikice da kuma nuna wariyar launin fata. Kuma, ya kamata a kara koyarwa al'ummomin kasa da kasa yadda za'a kafa wata makoma mai adalci, da mutunta juna, da kuma kare hakkin dan Adam. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China