Guterres ya fadawa 'yan jaridu cewa, suna maraba da namijin kokarin da kasar Sin ke yi wajen yaki da matsalar sauyin yanayi. Ya kara da cewa, tabbas matakan da kasar Sin din ke dauka za su yi matukar tasiri wajen samun bunkasuwar tattalin arzikinta.
Babban jami'in na MDD ya lura cewa, batun yarjejeniyar Paris da aka cimma game da sauyin yanayi ba lallai ne a iya aiwatar da ita yadda ya kamata ba, kuma batutuwan dake kunshe cikin yarjejeniyar ba za su wadatar ba wajen rage rumamar yanayin duniya a wannan karni zuwa kasa da maki biyu a ma'aunin Celsius, ko kuma kasa da maki 1.5 a ma'aunin Celsius.
Mista Guterres ya ce rawar da kasar Sin ke takawa a wannan fanni ya daga matsayin burin da ake da shi, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon tattaunawa masu yawa da aka yi da kuma karfafa hadin gwiwa da gwamnatin kasar Sin a wannan fanni. (Ahmad Fagam)