Yau Laraba ne a nan Beijing madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Sin na sa muhimmanci sosai kan tsaron lafiyar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, tana kuma goyon bayan MDD da ta dauki hakikanin matakai na kara tabbatar da tsaron lafiyar masu aikin kiyaye zaman lafiya.
Madam Hua ta fadi haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, dangane da rahoton da MDD ta kaddamar a kwanan baya kan tsaron lafiyar masu aikin kiyaye zaman lafiya. Madam Hua ta kuma nuna cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ta tura masu aikin kiyaye zaman lafiya kusan dubu 40 zuwa kasashe daban daban. Daga cikinsu akwai sojoji 13 da 'yan sanda 4 da suka rasa rayukansu yayin da suke aikin kiyaye zaman lafiya a ketare. (Tasallah Yuan)