in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi na'am da yadda zaben kasar Liberia ya gudana
2018-01-09 09:54:42 cri
Wata sanarwa ta kwamitin tsaron MDD ya fitar, ta bayyana gamsuwar mambobin kwamitin game da yadda zagaye na biyu na zaben kasar Liberia ya gudana cikin lumana.

Sanarwar ta rawaito mambobin kwamitin na tsaro na taya al'ummar kasar, da zababbiyar gwamnati, da 'yan siyasar kasar, da jam'iyyun gama kai, da 'yan jarida murnar gudanar da zaben na ranar 26 ga watan Disambar da ya gabata lami lafiya.

Har ila yau sanarwar ta jinjinawa 'yan takarar shugabancin kasar su biyu bisa dattaku da suka nuna yayin da suke yakin neman zabe. Kwamitin tsaron ya bayyana farin ciki bisa ci gaban da aka samu, na mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata cikin kwanciyar hankali bayan kusan shekaru sama da 70.

Kwamitin tsaron MDDr ya kuma jaddada muhimmancin sauyin gwamnatin da kasar ta samu bayan kammalar zabe, da tattaunawa tsakanin gwamnati mai barin gado da wadda ta gaje ta, matakin da ya kai ga rantsar da sabon shugaban kasar George Weah. (Saminu )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China