in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kiyaye tsaron kasa da kasa cikin hadin gwiwa shi ne babban tushen hana yaduwar makaman kare dangi, in ji wakilin Sin
2018-01-19 16:13:27 cri

Mukaddashin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana a yayin taron hana yaduwar makaman kare dangi da kwamitin sulhu na MDD ya shirya a jiya Alhamis cewa, hadin gwiwar samar da tsaro tsakanin kasashen duniya ita ce babbar hanyar hana yaduwar makaman kare dangi, kuma za a cimma wannan buri ne ta hanyar diflomasiyya.

Mr. Wu ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta goyon bayan yaduwar makaman kare dangi da yadda ake sufurin su a kasashen duniya. Kasar Sin ta sanya hannu kan dukkan yarjejeniyoyin hana yaduwar makaman kare dangi tare da shiga kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa. Haka kuma kasar Sin ta bullo da tsarin hana yaduwar makaman tare da tabbatar da cewa, ana martaba da dokokin da abin ya shafa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China