in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya ce ci rani na da alfanu ga ci gaban duniya
2018-01-12 11:00:27 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ja hankalin kasashen duniya, da su rika martaba 'yan ci rani, tare da kaucewa daukar matakan sanya shinge ga bakin haure dake shiga kasashe ta hanyar da doka ta tanada.

Antonio Guterres ya ce 'yan ci rani na taimakawa wajen daidaita tattalin arzikin duniya, suna rage gibi tsakanin kasashe mawadata da matalauta. Kaza lika suna kasancewa wata gada ta bunkasa cudanyar al'adu tsakanin sassa daban daban na duniya, baya ga daidaita yawan al'ummun duniya da suke yi.

Mr. Guterres wanda ya bayyana hakan yayin wani taron gama gari na MDDr, ya ce a zahiri ne, 'yan ci rani na bunkasa ci gaban duniya ta hanyar hidimomi da suke samarwa, da kuma kudade da suke aikewa kasashen su na asali. Ya ce bisa kididdiga, a shekarar da ta gabata ma'aikata 'yan ci rani sun aike da kudaden da yawan su ya kai ga dalar Amurka biliyan 600 zuwa kasashen su, adadin da ya rubanya daukacin tallafin da ake samarwa kasashen duniya har sau 3.

Babban magatakardar MDDr ya bukaci kasashen duniya da su karfafa dokokin su na baiwa bakin haure kariya, ta yadda za su amfana daga gudunmawar 'yan ci ranin, kana su ma bakin hauran su amfana yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China