in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar zazzabin cizon sauro babbar matsalar kiwon lafiya ce a fadin Afirka, in ji jami'in WHO
2018-01-27 13:20:50 cri
Jiya Jumma'a, wani jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana cewa, cutar zazzabin cizon sauro tana ci gaba da kasance matsalar kiwon lafiya mafi tsanani a kasashen Afirka.

Jami'in ya bayyana hakan ne a yayin taron koli na yaki da cutar zazzabin cizon sauro da aka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda mahalarta taron suka nuna damuwarsu kan yanayin yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka.

Shugaba mai kula da shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro na hukumar WHO Pedro Alonso, ya bayyana cewa, dukkan kasashen Afirka suna fuskantar matsalar yaduwar cutar zazzabin cizon sauro, kuma adadin masu kamuwar cutar ya fi yawa a Nijeriya da sauran kasashe na Afrikar.

Bisa rahoton cutar zazzabin cizon sauro na kasashen duniya na shekarar 2017 da hukumar WHO ta fidda, an ce, a halin yanzu, kasashe guda 15 ne suka fi fama da yaduwar cutar mafi tsanani, kuma adadin mutanen da suka kamu da cutar da kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar ya kai kashi 80 bisa dari a wadannan kasashe, kana kasashe 14 daga cikinsu daga nahiyar Afirka suke.

A yayin taron, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU, Moussa Faki, ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa, yaduwar cutar zazzabin cizon sauro ta kawo matsaloli da dama ga kasashen Afirka a fannonin kiwon lafiya, da raya tattalin arziki, da zamantakewar al'umma da dai sauransu.

Shi ya sa, ya yi kira ga mambobin kungiyar AU da su zuba jari a fannin kiwon lafiya, domin tabbatar da cimma nasarar yin kwaskwarima a kasashen Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China