Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, Daraktan sashen bada alluran rigakafi na Hukumar Lafiya ta Duniya Jean-MarieOkwo-Bele da kungiyar yaki da cutar kyanda ta Measles and Rubella Initiative, sun ce an samu raguwar mace-mace sanadiyyar cutar kyanda cikin shekaru 20 da suka gabata, amma a yanzu, dole ne aka kara jajircewa wajen fatattakarta baki daya.
Jean Okwo-Bele ya ce sai rigakafi ya isa ga ko wane yaro a ko ina, sannan za a yi nasarar fatattakar cutar.
Har yanzu akwai yara miliyan 20.8 da ba su karbi rigakafin cutar kyanda na farko ba, kuma sama da rabi na wadannan yara na kasashe 6 da suka hada da Nijeriya dake da miliyan 3.3 da Indiya dake da miliyan 2.9 yayin da Pakistan ke da miliyan 2.
Sauran su ne Indonesia mai miliyan 1.2 da Habasha dake da 900,000 da kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dake da 700,000. (Fa'iza Mustapha)