in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta gano magungunan magance cutukan Ebola da malaria
2018-01-20 13:02:02 cri

A jiya Jumma'a Najeriya ta ayyana cewa ta gudanar da wani bincike inda ta gano wasu magungunan gargajiya 6 wadanda za'a iya amfani da su wajen magance cutukan Ebola, da zazzabin malaria da ma wasu sauran cututtukan.

Karniyus Gamaniel, darakta janar na cibiyar binciken harhada magunguna ta Najeriya (NIPRD), shi ne ya tabbatar da hakan a Abuja, babban birnin kasar.

Ya ce cibiyar ta hada wani nau'in magani mai suna "NIPRIBOL", wanda za'a iya amfani da shi wajen kawar da kwayoyin cutar Ebola, ya kara da cewa, a halin yanzu cibiyar ta kammala kashin farko na yin nazari kan maganin.

Gamaniel ya ce, cibiyar ta kuma samar da nau'in magani na "NIPRIMAL", wanda za'a iya amfani da shi wajen magance cutar zazzabin cizon sauro wato malaria, ya kara da cewa mata masu juna biyu ma za su iya yin amfani da maganin ba tare da wata matsala ba.

Ya ce a halin yanzu, sun riga sun kammala wani shiri na samar da magungunan da kuma sayar da su a kasuwanni.

Ya ce, sun tsara tare da aiwatar da wasu tsare tare masu muhimmanci, wadanda suka hada da kafa wani tsari da yanayin aiki, da wasu tsare tsare na ilmi da kyakkyawan tsarin gudanarwa.

Gamaniel ya kara da cewa, sun gabatar da shirin amfani da magungunan gargajiya a tsarin kiwon lafiyar kasar da kuma kulla yarjejeniya da wasu kungiyoyin hada magunguna na cikin gida da na kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China