in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun UNICEF ya nuna damuwa kan yadda jama'a ke bahaya a fili a Najeriya
2017-11-23 10:09:53 cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF a takaice, ya bayyana jiya Laraba cewa, ya damu da yanayin tsaftar muhalli a Najeriya

Jami'in asusun na UNICEF mai kula da harkokin tsaftar ruwa, muhalli da kiwon lafiya a Najeriya (WASH) Zaid Jurji, ya ce daya bisa uku na 'yan Najeriya ne har yanzu ke bahaya a sararin Allah.

Jurji ya ce, wajibi ne a dauki matakan da suka dace don ganin an kawar da wannan tsohuwar al'ada. Don haka ya bukaci shugabannin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki, da su kara zage damtse wajen ilimantar da jama'a game da illolin dake tattare da wannan mummunar dabi'a.

Yanzu haka dai Najeriya ce kasa ta uku a duniya da har yanzu al'ummomin ta ke bahaya a filin Allah ta'ala.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China