in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ware ranar 12 ga watan Decemba matsayin ranar samun kiwon lafiya na bai daya ta duniya
2017-12-13 10:19:07 cri
MDD ta ayyana ranar 12 ga watan Decemba a matsayin ranar kiwon lafiya ta bai daya, ta na mai kira ga kasashe mambobinta su kara daura damarar tabbatar da kiwon lafiya ga kowa.

A wani kuduri da aka amince da shi a jiya, babban zauren MDD ya bukaci dukkan mambobin majalisar, su rika bikin ranar a kowacce shekara yadda ya kamata bisa muhimman batutuwan da suka shafesu, ta hanyar ilmantar da jama'a da gudanar da shirye-shirye, domin kara wayar da kai game da bukatar ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai isa ga kowa.

Zauren majalisar ya yi kira da a yi kokarin ganin dukkan mutane suna samun dama iri guda ta samun kiwon lafiya domin inganta matakan kariya da gyara da tunkarar cuttutuka dake kunshe cikin tsarin kiwon lafiya

Majalisar ta kuma yi kira da a kara kare lafiya da rayukan jami'an kiwon lafiya da masu aikin agajin jin kai, tare da kula da hanyoyin sumfurinsu da kayakin aiki da asibitoci, musammam a wuraren da ake rikici. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China