Mahukuntan kasar Sin sun lashi takwabin bullo da managartan matakai da nufin kara inganta sashen kiwon lafiyar kasar, ta yadda zai biya bukatun tsofaffin dake karuwa a fadin kasar.
Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan taron majalisar zartarwar kasar da firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, ta bayyana cewa, inganta sashen kiwon lafiya, wani muhimmin bangare ne na gyare-gyaren da mahukuntan kasar ta Sin ke aiwatarwa, da nufin biyan bukatun al'ummar Sinawa a bangaren kiwon lafiya.(Ibrahim)