Cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta fidda, ta kuma bayyana cewa birnin Afrin shine wani yankin dake karkashin ikon kasar Syria, matakan soja da kasar Turkiya ta dauka a wannan birnin sun keta ikon kasar Syria da kuma 'yancin kanta. Shi yasa, kasar Syria ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su yi Allah wadai kan matakan da kasar Turkiyar ta dauka, su kuma dauki matakai yadda ya kamata domin tsayar da matakan soja da kasar Turkiya take aiwatarwa a birnin Afrin mallakinta.
A ranar 20 ga wata, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da cewa, sojojin kasarsa zasu fara aiwatar da matakan soja a birnin Afrin dake arewacin kasar Syria.
Sa'an nan, a wannan rana da yamma, hedkwatar bada nasiha ga rundunonin sojojin kasar Turkiya ta bada sanarwa cewa, matakan sojan da kasarta ta dauka sun kasance "matakai ne na kare kanta bisa doka", kuma, kasar Turkiya tana mutunta ikon mulki da kuma 'yancin kan kasar ta Syria. (Maryam)